IQNA

Siyarar Adawa Da HKI Ta Ordogon Ta Yi Sanadiyar Karuwar Farin Jininsa

11:47 - June 17, 2010
Lambar Labari: 1941445
Bangaren siyasa da zamantakewa; muassisar da ke gudanar da bincike kan tattalin arziki da zamantakewa a kasar Turkiya ta gudanar da kuri'ar jin ra'ayin jama'a kan fuskantar Haramtaciyar kasar isra'ila da Ordogon ke yi da adawa da siyasar mamay ta gwamnatin Haramtacciyar kasar Isra'ila shi ne babban dalili karuwar farin jinin Turkiya a duniyar larabawa.
Cibiyar da ke kula da harkokin kur'ani a nan jamhuriyar Musulunci ta Iran Ikna daga resshenta na kasar Turkiya bayan ta nakalto daga jaridar Alyaum Alsa'in ta kasar Masar ta watsa rahoton cewa; muassisar da ke gudanar da bincike kan tattalin arziki da zamantakewa a kasar Turkiya ta gudanar da kuri'ar jin ra'ayin jama'a kan fuskantar Haramtaciyar kasar isra'ila da Ordogon ke yi da adawa da siyasar mamay ta gwamnatin Haramtacciyar kasar Isra'ila shi ne babban dalili karuwar farin jinin Turkiya a duniyar larabawa. Ita wannan kuri'ar jin ra'ayin jama'a an gudanar da ita a cikin kasashe bakwai na kasashen larabawa Masar,Suriya,Labanon,Jodan,Palasdinu,Iraki da Saudiyainda Turkiya a karkashin mulkin jam'iyar Adalci da ci gaban Musulunci ta Turkiya da Ordogon ke jagoranta ta zama kasa mafi soyuwa a tsakanin duniyar Larabawa.


598330

captcha