IQNA

An Buga Littafin 'Yanci A Mahangar Kur'ani Mai Tsarki

14:50 - June 17, 2010
Lambar Labari: 1941532
Bangaren kasa da kasa; An buga littafin matsayin 'yanci a mahangar kur'ani mai tsarki, wanda malamin shi'ar nan na kasar Saudiya Sayyid Hasan Namir Ya rubuta kuma aka buga shi a Labanan.
Kamfanin dillancin labaran iqna ya nakalto daga kamfanin dillancin labaran kur'ani na Muzn cewa, an buga littafin matsayin 'yanci a mahangar kur'ani mai tsarki, wanda malamin shi'ar nan na kasar Saudiya Sayyid Hasan Namir Ya rubuta kuma aka buga shi a Labanan. Bayanin ya ci gaba da cewa Sayyid Namir ya yi kokari a cikin littafin ya bayyana mahangar kur'ani dangane da abin da ake kira 'yanci, da kuma matsayin mutum a cikin rayuwar zamantakewa. Malamin dai shi ne limamin masallacin juma'a na garin Saihat a kasar Saudiyya. 598878


captcha