IQNA

Wata Kunya Farar Hula A Birtaniya Za Ta Kai Karar Isra'ila A Kotu

14:47 - June 17, 2010
Lambar Labari: 1941534
Bangaren kasa da kasa; Wata kungiyar farar hula mai zaman kanta a kasar Birtaniya za a ta karar Isra'ila a kotun Birtaniya kan kai hari a kan masu kai agaji Gaza a cikin ruwa na kasa da kasa.
Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa, a wani labari da ya nakalto daga shafin yanar gizo na haber an habarta cewa, Wata kungiyar farar hula mai zaman kanta a kasar Birtaniya za a ta karar Isra'ila a kotun Birtaniya kan kai hari a kan masu kai agaji Gaza a cikin ruwa na kasa da kasa. Bayanin ya ci gaba da cewa wannan kungiya ta kudiri aniyar gurfanar da manyan jami'an haramtacciyar gwamnatin Isra'ila a gaban kuliya da nufin hukunta su kan ayyukan ta'addanci da dabbancin da suka aikata na kai hari kan fararen hula a lokacin da suke cikin ruwa na kasa da kasa da nufin kai taimakon kayan abinci da magunguna ga al'ummar Gaza. 598853



captcha