IQNA

Shrin Horar Da Matasa Ilimin Musulunci A Birnin Sharjah

14:49 - June 17, 2010
Lambar Labari: 1941536
Bangaren kasa da kasa; Hukumar kula da harkokin addinin musulunci da birnin Sharjah ta sanar cewa a cikin wannan bazarar za a gudanar da shirin horar da matasa ilmin addinin musulunci.
Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa, a wani rahoto da yanakalto daga kamfanin dillancin labaran hadaddiyar daular larbawa wam an bayyana cewa, hukumar kula da harkokin addinin musulunci da birnin Sharjah ta sanar cewa a cikin wannan bazarar za a gudanar da shirin horar da matasa ilmin addinin musulunci. Rahoton ya ce a yayin bayar da horon za a koyar da matasan ilmomin fikihu kur'ani akida kyawawan dai'u da dai sauransu, kuma za a gayyaci malamai domin gabatar musu da laccocin fadakarwa. 598614
captcha