Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa, kamfanin dillancin labaran kuna na kasar Kuwait ya habarta cewa, an fara gudanar da ginin wata babbar cibiyar koyar da karatun kur'ani mai tsarki a kasar Kuwait, wadda aka baiwa suna Assalam a cikin salam da ke birnin Kuwait. Bayanin ya ci gaba da cewa Mataimakin fira ministan kasar kuma ministan mai kula da harkokin musulunci a kasar Rashid Abdulmuhsin Hammad ya bayyana cewa suna goyon bayan gina wannan cibiya kuma za su bayar da dukkanin taimako. 598470