Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa, a wani bayani da ya nakalto daga shafin yanar gizo na moralhaber an bayyana cewa, an rufe wata makarantar musulmi a kasar Holland saboda rashin samun taimako daga gwamnatin kasar ta bangaren ayyukan da ake yi na kudi a makarantar. Bayanin ya ce mahukuntan kasar sun ce ba za su bayar da taimakon kudi ga makarantar ba wadda ta sakndare ce har sai dalibanta sun kai 757, amma kasantuwar daliban ba su kai haka ba ba za su samu taimakon gwamnati ba. 598480