IQNA

Musulmin Duniya Ba Su Dogaro Da Shugaban Amerika

11:21 - June 19, 2010
Lambar Labari: 1942142
Bangaren kasa da kasa;karkashin jin ra'ayin jama'a da cibiyar Pew Research Center ta gudanar sanakamakon ya nuna musulmin duniya bas u dogaro da siyasar shugaban kasar Amerika Barack Obama kuma sun komo daga yin dogaro ne da siyasarsa kafin zabarsa.
Cibiyar da ke kula da harkokin kur'ani a nan jamhuriyar Musulunci ta Iran ikna bayan ta nakalto daga jaridar Zaman a kasar turkiya ta watsa rahoton cewa;
karkashin jin ra'ayin jama'a da cibiyar Pew Research Center ta gudanar sanakamakon ya nuna musulmin duniya bas u dogaro da siyasar shugaban kasar Amerika Barack Obama kuma sun komo daga yin dogaro ne da siyasarsa kafin zabarsa.Sakamakon jin ra'ayin jama'a da cibiyar Piyo ta gudanar a watanni biyu da suka gabata a cikin kasashe ashirin da daya na duniya bakwai daga cikinsu kasashen musulmi ne na nuni da cewa; kawai kaso ashirin da bakwai na al'ummar Masar,Turkiya Da Pakistan suke dogaro da siyasar Obama. Kuma sakamakon ya kara nuni da cewa a kowace rana ta Allah farin jinin Obama a tsakanin kasashen musulmi raguwa yake yi kuma suna ganin Amerika na kara zama babban hhadri ga duniya.

599539
captcha