Kamfanin dillancin labaran iqna ya hbarta cewa, a wani bayanin da ya nakalto daga bangaren yada labarai na ISESCO an bayyana cewa, babban sakataren kungiyar yada al'adu ta kasashen musulmi Abdulaziz Tuwaijari ya tabbatar da cewa Isra'ila ta gurbata siyasa tsakanin Amurka da kasashen musulmi. Ya bayyana hakan ne a cikin wani bayani da kungiyar ta fitar dangane da zaman taron da za a gudanar tsakanin Amurka da kasashen musulmi, inda ya ce babu wani canji da musulmi suka gani a cikin bayanan da Obama ya yi ga duniyar musul shekarar da ta gabata, dangane da goyon bayan ayyukan ta'addancin da Isra'ila take yi kan musulmi. 599656