Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa, a wani rahoto da ya nakalto daga shafin yanar gizo na ucide an bayyana cewa, Wadanda suka halarci taron tattalin arzikin kasashen musulmi a birnin Madrid da rawarsa a duniya sun bayyana cewa zai iya taimaka ma tattalin arzikin kasar Spain. Taron wanda ya samu halartar masana harkokin tattalin arziki daga kasashen musulmi da kuma jami'an gwamnatin Spain, ya mayar da hankali ne kan yadda bangarorin kasashen musulmi da kuma Spain za su karfafa dangantakarsu ta tattalin arziki. 599646