Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa, a cikin wani rahoto da kamfanin dillancin labaran kasar Faransa AFP ya bayar an bayyana cewa, An rattaba hannu kan wata takardar yarjejeniyar fahimtar juna tsakanin gwamnatin Faransa da kuma majalisar kungiyoyin mabiya addinin musulunci da ke kasar. Bayanin ya ci gaba da cewa a cikin yarjejeniyar dukkanin bangarorin biyu sun amince da kawo karshen nuna wariyar da ake yi ga musulmi a kasar, tare da yin kalamai na batunci ga addinin musulunci. 599556