IQNA

Larjani Zai Halarci Taron Majalisun Kasashen Musulmi A Suriya

16:54 - June 20, 2010
Lambar Labari: 1943271
Bangaren siyasa : Ali Larjani shugaban majalisar dokokin jamhuriyar Musulunci a cikin yan kwanaki masu zuwa na tara da goma ga watan Tir na wannan shekara zai kasance a kasar Suriya domin halartar taron majalisun kasashen musulmi da za a gudanar a wannan kasa.

Cibiyar da ke kula da harkokin kur'ani a nan jamhuriyar Musulunci ta Iran Ikna ta watsa rahoton cewa; Ali Larjani shugaban majalisar dokokin jamhuriyar Musulunci a cikin yan kwanaki masu zuwa na tara da goma ga watan Tir na wannan shekara zai kasance a kasar Suriya domin halartar taron majalisun kasashen musulmi da za a gudanar a wannan kasa. Husein Sheikul Islam mai bawa shugaban majalisar shawara ta jamhuriyar Musulunci ta Iran a wata tattaunawa day a yi da cibiyar da ke kula da harkokin kur'ani a nan Iran ya bada wannan labarin.Kuma shugabannin majalisun kasashen musulmi za su tattaunawa ne kan harin da sojojin gwamnatin haramtaciyar kasar Isra'ila suka kai wa tawagae=r ayarin kungiyar hakkin dan adam masu kokarin kawo karshen killacewa da haramtaciyar kasar Isra'ila ta yi wa yankin zirin gaza.


600232

captcha