IQNA

A Labanon An Fadada Cibiyar Yada Addini Musulunci Ta Aziz

16:53 - June 20, 2010
Lambar Labari: 1943276
Bangaren siyasa da zamantakewa; a ranar ashirin da takwas ga watan Khurdad na wannan shekara ta dubu daya da dari uku da tamanin da tara hijira shamsiya a kasar Labanon an fada cibiyar yada addinin Musulunci ta Aziz a kauyen G+Fanidik a lardin Akar da ke arewacin Labanon.

Cibiyar da ke kula da harkokin kur'ani a nan jamhuriyar Musulunci ta Iran Ikna daga reshenta a kasar labanon ta watsa rahoton cewa; a ranar ashirin da takwas ga watan Khurdad na wannan shekara ta dubu daya da dari uku da tamanin da tara hijira shamsiya a kasar Labanon an fada cibiyar yada addinin Musulunci ta Aziz a kauyen G+Fanidik a lardin Akar da ke arewacin Labanon. A wajen bukin bude wannan cibiya an samu halartar Khalid Zahriman wakilin firaminitan kasar Labanon Sa'ad Hariri da kuma Sheikh Amin Alkirdi wakilin Muhammad Rashid Kabani babban mai bada fatawa a kasar labanon da kuma shugabanin al'adu da magadayyan gari da malamai a kasar ta labanon.


600113
captcha