Bangaren adabi : a karon farko an fara taron marubuta na kasashen musulmi kuma an fara wannan taro ne a ranar talatin ga watan Khurdad wato yau ken an tare da jawabin Mahmud Ahmad Najad .
Cibiyar da ke kula da harkokin kur'ani a nan jamhuriyar Musulunci ta Iran Ikna ta watsa rahoton cewa;
a karon farko an fara taron marubuta na kasashen musulmi kuma an fara wannan taro ne a ranar talatin ga watan Khurdad wato yau ken an tare da jawabin Mahmud Ahmad Najad . Kuma da misalin karfe takwas da mintoci goma sha biyar ne aka bude wannan taro tare da jawabin shugaban kasar iran Mahmud Ahmad Najad kuma za a ci gaba da gudanar da wannan taro har zuwa goma talatin da daya ga watan na Khurdad inda marubuta kimanin sattin daga kasashen talatin daban daban suka halarta da suka hada kasashen Azarbaijan,Uzbakistan,Afganistan, iHadeddiyar daulkar larabawa,Indonosiya, Bangladesh,Pakistan, Tajikistan, Turkimanistan,Turkiya, Cin,Suriya,Iraki,Saudiya, Mauritaniya, Bosniya Herzegobin,Raha,Faransa,Afrika ta kudu, Masar, najeriya, Tanzaniya, Etiophiya,Ghana da Keniya.
600033