Cibiyar da ke kula da harkokin kur'ani a nan jamhuriyar Musulunci ta Iran Ikna bayan ta nakalto daga Yeni Safak ta watsa rahoton cewa; Mahardata Kur'ani Mai girma a birnin Istambul na kasar Turkiya a yau ne talatin ga watan Khurdad a masalacin Fatih suka gudanar da taro a tsakaninsu. Su dai wadannan mahardata kur'ani sun fit one daga fadin kasar ta Turkiya inda za su tattauna a tsakaninsu da yin nazarin hanyoyin da za su kara inganta hardar kur'ani da magance wasu matsaloli da ke kawo masu cikas.
599796