IQNA

Siyasar Kasar Amurka Ta Waje Ta Ginu Ne Kan Alkawali Da Sabawa

18:39 - June 20, 2010
Lambar Labari: 1943315
Bangaren siyasa; Ministan tsaron kasar Iran janar Wahidi ya bayyana cewa siyasar Amurka ta waje ta ginu kan daukar alkawulla da kuma saba su domin maslahar kanta kawai.
Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa, a wani rahoto da ya nakalto daga shafin yanar gizo na ma'aikatar tsaron Jamhuriyar Musulunci ta Iran an bayyana cewa, ministan tsaron kasar Iran janar Wahidi ya bayyana cewa siyasar Amurka ta waje ta ginu ne kan daukar alkawulla da kuma saba su domin maslahar kanta kawai. Ya ci gaba da cewa furucin day a fito daga bakin wasu jami'an gwamnatin Amurka kan makamai masu linzami da Iran take mallaka, da cewa barazana ne ga turai, ya ce wanna shafci fadi ne kawai, domin kuwa dukkanin makaman Iran masu linazami na kariyar kai ne.600259



captcha