Bangaren fikira da ilimi; Bangaren yada al'adu da ilimi na kasar Iran a kasar Canada zai shirya taron maulidin Imam Ali (AS) a cikin mako mai zuwa a karamin ofishin jakadancin kasar.
Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa, bangaren yada al'adu da ilimi na kasar Iran a kasar Canada zai shirya taron maulidin Imam Ali (AS) a cikin mako mai zuwa a karamin ofishin jakadancin kasar. Bayanin ya kara da cewa wannan na daya daga cikin irin tarukan da ofishin kan shirya domin kara fadakar da musulmi matsayin iyalan gidan manzon Allah (SAW) da kuma darussan da za a dauka daga rayuwarsu.600345