IQNA

Duniya Na Ta Kara Fadaka Kan Ta'addancin Isra'ila

18:41 - June 20, 2010
Lambar Labari: 1943321
Bangaren siyasa; Harin ta'addanci da dabbancin da haramtacciyar kasar Isra'ila ta kai kan masu kai agaji a zirin Gaza ya kara fitar da surarta duniya kowa ya gani.
Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa, shafin yanar gizo na ma'aikatar harkokin cikin gida a Iran ya habarta cewa, minister mai kula da harkokin cikin Mustafa Najjar ya bayyana cewa, harin ta'addanci da dabbancin da haramtacciyar kasar Isra'ila ta kai kan masu kai agaji a zirin Gaza ya kara fitar da surarta duniya kowa ya gani. Ya ci gaba da cewa ko shakka babu rashin basirar yahudawan sahyuniya da girman kansu shi ne babban abin zai kawo karshensu, wanda kuma ayyukan ta'addancin da suka aikata a cikin 'yan lokutan sun kara bayyana matsayinsu a duniya. 600282



captcha