Bangaren fikira da ilimi; Shugaban cibiyar yada al'adu da ilimi ta kasar Iran kuma mamba a majalisar tsara kundin tsarin mulki ya bayyana cewa dole a samu dangantaka tsakanin madaba'antun Musulunci.
Kamfanin dilalncin labaran iqna ya nakalto daga bangaren sadarwa na taron kasa da kas ada ake gudanarwa na madaba'antun kasashen musulmi cewa, shugaban cibiyar yada al'adu da ilimi ta kasar Iran kuma mamba a majalisar tsara kundin tsarin mulki Madi Mustafavi, ya bayyana cewa dole a samu dangantaka tsakanin madaba'antun Musulunci. Ya ci gaba da cewa ta hanyar fahimtar juna da hadin gwina ne kawai madaba'antun kasashen musulmi za su iya samun damar isa da sakonni ga duniya baki daya kan manufofin addinin Musulunci.600262