Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa, a wani labari da ya nakalto daga jaridar Ukaz ta kasar Saudiyya an habarta cewa, za a bude wani dakin ajiye kayan tarihi na suka danganci ita ce da tsirrai da aka mabata a cikin kur'ani mai tsarki, wanda za a bude a birnin Makka mai alfarma. Bayanin ya ci gaba da cewa wannan dakin kayyakin tarihi zai kunshi dukkanin itace da tsirrai da aka ambata a cikin kur'ani. 600068