IQNA

Malaman makaranta A Girka Za Su Gyara Wata Makaranta A Gaza

19:53 - June 20, 2010
Lambar Labari: 1943336
Bangaren kasa da kasa; Kungiyar malaman makarantun sakandare na kasar Girka za su gyara wata makaranta a yankin zirin Gaza a garin Jabalia da ke arewacin yankin.
Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa, ya nakalto daga shafin sadarwa na jazeera net cewa, kungiyar malaman makarantun sakandare na kasar Girka za su gyara wata makaranta a yankin zirin Gaza a garin Jabalia da ke arewacin yankin. Bayanin ya ci gaba da cewa wannan makaranta za a gyara ta ne domin nuna goyon baya ga al'ummar yanki da suke karkashin danniyar yahudawan sahyuniya. 599954




captcha