Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa, a wani labarin da ya nakalto daga banagaren yada labarai na jami'ar Azhar an bayyana cewa, babban malamin jami'ar azhar da ke birnin Alkahira ta kasar Masar ya sanar da mazhabar shi'a a matsayin daya daga cikin mazhabobin addinin muslunci. Bayanin ya ci gaba da cewa wannan mataki da shugaban jamia'r ya dauka ya bakantawa malaman wahabiyawan Saudiyya rai, inda wasu daga cikinsu suka kalubalance amma bai janye daga matsayinsa ba. 599912