IQNA

Cibiyar Kur'ani Ta Dammam Tana Daukar Mata Mahardata 'Yan Shi'a

14:38 - June 21, 2010
Lambar Labari: 1943848
Bangaren kasa da kasa; Cibiyar kur'ani mai tsarki ta yankin Dammam a kasar Saudiyya tana daukar mata mahardata kur'ani mabiya mazhabar shi'a a yankin domin shiga cikin ayyukanta.
Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa, a wani labari da ya nakalto daga kamfanin dillancin labaran Muzn an bayyana cewa, cibiyar kur'ani mai tsarki ta yankin Dammam a kasar Saudiyya tana daukar mata mahardata kur'ani mabiya mazhabar shi'a a yankin domin shiga cikin ayyukanta. Bayanin ya ci gaba da cewa wannan cibiya za ta fara gudanar da wani shiri na horar da mata mahardata kur'ani mai tsarki, inda shirin wannan horo zai kwashe kimanin wata daya ana gudanar da shi. 601171


captcha