IQNA

An Fara Gudanar Da Zaman Kwamitin Majalisun Kasashen Musulmi

14:39 - June 21, 2010
Lambar Labari: 1943849
Bangaren kasa da kasa: An fara gudanar da zaman kwamitin majalisun kasashen musulmi, wanda shi ne karo na 23 da ake gudanar da irinsa a birnin Dubai na hadaddiyar daular larabawa.
Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa, a wani labari da ya nakalto daga kamfanin dilalncin labaran wam na kasar hadaddiyar daular larabawa an habarta cewa, yanzu haka an fara gudanar da zaman kwamitin majalisun kasashen musulmi, wanda shi ne karo na 23 da ake gudanar da irinsa a birnin Dubai na hadaddiyar daular larabawa. Bayanin ya ci gaba da cewa taron an samun halartar wakilai daga kasashe daban-daban da suka hada da Masar, Aljeria, Iran, Saudiyya,Indonesia, Uganda, Turkiya, kamerun da Burkinafasso. 601147



captcha