IQNA

Shirin Bayar Da Horon ilimin Musulunci Ga Daliban makarantun Kuwait

14:37 - June 21, 2010
Lambar Labari: 1943859
Bangaren kasa da kasa; Za a fara gudanar da shirin na bayar da horo na musamman kan ilmomin addinin Musulunci ga daliban makarantu a Kuwait a karo na goma sha bakawai.
Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa, a wani rahoto da ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo na Arab Timesonline an bayyana cewa, za a fara gudanar da shirin na bayar da horo na musamman kan ilmomin addinin Musulunci ga daliban makarantun sakandare na kasar Kuwait a karo na goma sha bakawai. Wannan shiri dai an saba gudanar shi a kowace shekara a lokutan hutun bazaar, wanda wanna shi ne karo na goma sha bakwai da za a gudanar da shi kamar yadda ma'aikatar ilimi da cibiyar kula da harkokin addinin Musulunci ta kasar suka shirya gudanarwa. 600706


captcha