Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa, jaridar Jordan Times da ake bugawa a birnin Aman fadar mulkin kasar Jordan ta habarta cewa, a cikin wannan shekarar nan aka fara gina wata babbar cibiyar bude ido ta musulunci a kasar Jordan a gefen kogin kasar, wanda zai lashe tsabar kudi dalar Amurka miliyan dari daya. Bayanin ya ci gaba da cewa wannan cibiya za ta zama irinta ta farko da za a gina kasar, wadda za ta kunshi abubuwa na bude amma na musulunci, da suka hada da kayyakin tarihi da kuma hotunan muhimman wurare gami da zane-zane na addinin musulunci. 600658