Bangaren al'adu da fasaha; a ranar ashirin da hudu ga watan Khurdad ne aka fara gudanar da makon al'adu na Iran a birnin Minisk babban birnin kasar Balarus inda aka samu halartar masana fasaha kimanin hamsin kuma a jiya ne aka kawo karshen wannan mako na al'adun Iran.
Cibiyar da ke kula da harkokin kur'ani a nan Jamhuiyar Musulunci ta Iran Ikna daga reshen cibiyar da ke hukumar al'adu da kusanci a tsakanin musulmi ta Iran ta watsa rahoton cewa; a ranar ashirin da hudu ga watan Khurdad ne aka fara gudanar da makon al'adu na Iran a birnin Minisk babban birnin kasar Balarus inda aka samu halartar masana fasaha kimanin hamsin kuma a jiya ne aka kawo karshen wannan mako na al'adun Iran. A cikin wannan mako an baje kolin abubuwa uku masu take mace ba'iraniya,Iran a yau da kuma darduma ta Iran.
601132