IQNA

Za A Gudanar Da Bukin Dora Tubalin Gina Cibiyar Kur'ani A Kuwait

18:52 - June 21, 2010
Lambar Labari: 1944061
Bangaren kasa da kasa; Za a gudanar da wani bukin dora tubalin gina wata babbar cibiyar harkokin kur'ani mai tsarki da aka sama suna Alsabahiyya a Kasar Kuwait.
Kamfanin dilalncin labaran iqna ya nakalto daga daga jaridar kasar Kuwait Alkabs cewa, a cikin makon nan ne za a gudanar da wani bukin dora tubalin gina wata babbar cibiyar harkokin kur'ani mai tsarki da aka sama suna Alsabahiyya a Kasar Kuwait. Ministan ma'aikatar kula da harkokin addinin musulunci ta kasar ne Adil Fala zai jagoranci gudanar da shirin bude cibiyar. Bayanin ya ci gaba da cibiyar za ta mayar da hankali ne wajen horar da matasa karatun kur'ani mai tsarki da ma sauran ilmomin musulunci. 600631



captcha