IQNA

An Fara Gudanar Da Shrin Koyar Da Hardar Kur'ani A Kutaif

18:52 - June 21, 2010
Lambar Labari: 1944062
Bangaren kasa da kasa; An fara gudanar da wani shiri na koyar da yara matasa hardar kur'ani mai tsarki da kuma ilmin ka'idojinsa wato tajwid a yankin Kutaif na kasar Saudiyya.
Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa, a wani labari da ya nakalto daga shafin kamfanin dillancin labaran kur'ani na muzn an bayyana cewa, an fara gudanar da wani shiri na koyar da yara matasa hardar kur'ani mai tsarki da kuma ilmin ka'idojinsa wato tajwid a yankin Kutaif na kasar Saudiyya, wanda aka saba gudanar da irinsa a kowace shekara a lokutan bazara. Bayanin ya ci gaba da cewa a cikin shirin bayar da horon za a hada da koyar da ilmomin akida da fikihu addu'oi da dai sauransu, domin ba yaran cikakken horo na sanin addini. 600631

captcha