IQNA

Zanagar-Zangar Kalubalantar Dokar Hana Saka Hijabi A Kosovo

18:52 - June 21, 2010
Lambar Labari: 1944064
Bangaren siyasa da zamantakewa; Dubban musulmi ne suka gudanar da gagarumar zanga-zanga a Kosovo don nuna rashin amincewa da dokar hana saka hijabi.
Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa, a wani labari da ya nakalto daga bangaren yada labaransa a yankin Balkan an bayyana cewa, dubban musulmi ne suka gudanar da gagarumar zanga-zanga a birnin Prishtina na kasar Kosovo, biyo bayana kafa dokar hana saka hijabi a kasar. Bayanin ya ci gaba da cewa dubban musulmin da suka gudanar da jerin gwamnon sun yi tarera take da ke neman gwamnatin kasar ta janye batun kafa dokar da ta hana saka hijabin musulunci a cikin makarantun kasar, tare da bayyana hakan a matsayin danne hakkokin musulmi.601002


captcha