Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa, a wani labari day a nakalto daga bangaren yada labaransa na kasar Jordan an habarta cewa, ministan ma'ikatar kula da harkokin addinin muslunci na kasar Jordan Abdulsalam Ibadi ya bayyana cewa, ya zuwa yanzu sama da dalibai dubu 250 suka yi rijista a makarantu da cibiyoyin hardar kur'ani mai tsarki a kasar Jordan, domin shiga cikin shirin bayar da horon hardar kur'ani na wannan bazara. Ya ce yanzu haka an fara gudanar da shirin wanda zai kwashe tsawon wata guda. 600959