Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa, shafin sadarwa na sbpost cewa, wani malamin jami'ar Dublin Aiman Walsh ya bayayna cewa, Ireland na bukatar sanin tsari tattalin arzikin Musulunci domin ta yi amfani da shi wajen gyara harkokin tattalin arzikinta. Bayanin ya ci gaba da cewa malamin jami'ar ya jadda muhimmancin yin nazari kan tsarin tattalin arziki ga gwamnatin Ireland, wanda a cewarsa hakan zai bayar da dama wajen warware da dama daga cikin matsalolin tattalin arzikin da take fama da shi. 601637