Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa, a wani labari da ya nakalto daga jaridar raya da ake buga a birnin Doha an habrta cewa, a karon farko za a gudanar da wata gasa ta ilmomin kur'ani a kasar katar da za a shafi bangarori tafasiri da kuma dalilan safkar ayoyi bisa ruwayoyin hadisi. Bayanin ya ci gaba da cewa a gasar za a rika gudanar da tambayoyi ne kan lamurra da suka shafi bangarori na ilimin kur'ani, da ma karatun wasu ayoyi da surorin da suke ciki a wasu lokuta. Rahoton ya ce tuni cibiyoyin kur'ani suka fara shirin shiga wannan babbar gasa da za a gudanar a kasar. 601521