Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa, a wani labari da ya nakalto daga shafin yanar gizo na jaridar albilad ta kasar Saudiyya an habarta cewa, kwamitin kula da harkokin kur'ani da harda gami da shirya gasa a birnin Jidda na kasar saudiya na bayar da takardun shedar kwarewa ga dalibai da kuma malaman kur'ani. Bayanin ya ci gaba da cewa akawai ka'idoji da kwamitin kan kiyaye kafin bayar da irin wadannan takarudun sheda ga dalibai ko malaman da suke koyar da karatu ko harder kur'ani mai tsarki. 601494