IQNA

An Kammala Shirin Bayar Da Horon Karatun Kur'ani A Burnai

13:36 - June 22, 2010
Lambar Labari: 1944549
Bangaren kasa da kasa; An kammala wani sabon shiri da aka bullo da shi na bayar da horon karatun kur'ani mai tsarki ga ma'aikatan gidan kaso a tsibirin Burnai.
Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa, a wani rahoto da ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo na Bruneionline an habarta cewa, yanzu haka dai an kammala wani sabon shiri da aka bullo da shi na bayar da horon karatun kur'ani mai tsarki ga ma'aikatan gidan kaso a tsibirin Burnai. Bayanin ya ci gababda cewa a cikin wannan horo da aka bayar na tsawon wata guda, dukkanin ma'aikatan gidan kaso a tsibirin Burnai sukan karanta kur'ani baki da safe kafin fara ayyukansu a gidajen kaso. An gudanar da shirin ne da nufin koyar da su ladubba da kuma sanin yadda ya kamata su mu'amala da fursunoni bisa koyarwa irin ta Musulunci. 601494




captcha