Kamfanin dilalncin labaran iqna ya habarta cewa, a wani labari da ya nakalto daga shafin sadrwa na beyazgazet an habarta cewa, an gudanar da gasar karatun kur'ani mai tsarki ta kasa baki daya a matakin karshe a kasar Turkiya, wadda aka gudanar a birnin Azmir dake kasar. Bayanin ya ci gaba da cewa bayan kamamla gasar, Yunus Emre Demir ya samu lashe gasar tare da samun kyauta ta fiyayyen makarancin kur'ani mai tsarki. 601521