Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa, a wani bayani da ya nakalto daga bangaren yada labaransa da ke yankin gabacin Asia an habarta cewa, daya daga cikin malaman addinin Musulunci a kasar sri lanka sheikh Muhammad Zainuddin Arif ya bayyana cewa ana fama da karancin tarjamar kur'ani. Bayanin ya ci gaba da cewa malamin ya yi korafi ga bangarorin da suke kula da harkokin tarjama a kasashen musulmi, da su mayar da hankali wajen samar da kur'anai da aka tarjama a cikin harshen Tamil, saboda karancinsa a yankunan da ake yin amfani da shi. 601504