Cibiyar da ke kula da harkokin kur'ani a nan jamhuriyar Musulunci ta Iran Ikna daga reshenta da ke hukumar yada al'adun Jamhuriyar Musulunci ta Iran a ketare da kuma kara kusanci a tsakanin kasashen musulmi da musulmin duniya ta watsa rahoton cewa; ofishin da ke kula da harkokin al'adun Iran a Rasha a lokacin ganawarsa da muftin jamhuriyar Bashkiristan ya bayyana masa aniya da shirin Iran na fadada dangantakarta ta al'ada irin ta Musulunci da jamhuriyar Bashkiristan.Abu Zar Ibrahimi Turkiman mai kula da ofishin yada al'adun Iran a kasar Rasha a lokacin ganawarsa da Nur Muhamma muftin jamhuriyar Bashkiristan ya yi masa wannan bayani.
601622