Cibiyar da ke kula da harkokin kur'ani a nan jamhuriyar Musulunci ta Iran Ikna daga reshenta da ke hukumar yada al'adun Jamhuriyar Musulunci ta Iran a ketare da kuma kara kusanci a tsakanin kasashen musulmi da musulmin duniya ta watsa rahoton cewa; a ranar laraba biyu ga watan Tir a birnin Tehran za a gudanar da bukin bude darul Kur'ani dubu uku da ministan ilimi da tarbiya zai kaddamar a dakin al'adu. Wadannan darul Kur'ani an ware sun e a cikin hutun karshen shekara domin bawa yara kanana damar yin karatu.
601727