Bangaren kasa da kasa; ga masu sha'awar shiga a dama da su a cikin kasuwar baje koli karo ta biyu ta kasa da ksa ta gwagwarmayar Musulunci da zummar fadada al'adar gwagwarmaya da tasirin sadaukar da kai a yankin suna iya aikewa da makalolinsu har zuwa ranar goma ga watan Tir na wannan shekara ta dubu daya da dari uku da tamanin da tara hijira shamsiya.
Cibiyar da ke kula da harkokin kur'ani a nan jamhuriyar Musulunci ta Iran Ikna daga reshenta da ke hukumar yada al'adun Jamhuriyar Musulunci ta Iran a ketare da kuma kara kusanci a tsakanin kasashen musulmi da musulmin duniya ta watsa rahoton cewa; ga masu sha'awar shiga a dama da su a cikin kasuwar baje koli karo ta biyu ta kasa da ksa ta gwagwarmayar Musulunci da zummar fadada al'adar gwagwarmaya da tasirin sadaukar da kai a yankin suna iya aikewa da makalolinsu har zuwa ranar goma ga watan Tir na wannan shekara ta dubu daya da dari uku da tamanin da tara hijira shamsiya. A wajen wannan baje koli ya shafi fina-fina da sinima da fasaha. Masu Son Karin bayani na iya bugawa kan wannan lamba: 021-22088571
601699