IQNA

Malaman Azhar Ba Su Amince Da Karatun Mata Radiyo Da Talabijin Ba

15:44 - June 23, 2010
Lambar Labari: 1945453
Bangaren kasa da kasa; Wasu daga cikin manyan malaman jami'ar Azhar ta kasar Masar sun ki amincewa da karatun kur'anin da mata ke yi a cikin gidajen radiyo da talabijin.
Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa, a wani labari da ya nakalto daga jaridar kasa da kasa sharq alausat an bayyana cewa, wasu daga cikin manyan malaman jami'ar Azhar ta kasar Masar sun ki amincewa da karatun kur'anin da mata ke yi a cikin gidajen radiyo da talabijin. Bayanin ya ci gaba da cewa malaman sun yi dogaro ne da wasu dalilai da suka dogara da su an shari'a wajen fitar da wannan hukunci, amma wasu daga cikin malaman jami'ar ba su ce komai kan wannan mas'ala ba. 602651



captcha