Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa, a wani rahoto da ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo na ice-el an bayyana cewa, za a gudanar da tarukan maulidin Imam Ali (AS) a babban dakin karatun cibiyar Musulunci ta kasar Birtaniya da ke birnin London fadar mulkin kasar. Taron zai samu halartar mabiya mazhabar iyalan gidan manzon Allah (SAW) daga sassa daban-daban na kasar Birtaniya, inda za a gabatar da jawabai dangane sirar Imam Ali (AS) da kuma wasu daga cikin darussan dake cikin rayuwarsa mai albarka da dukkanin musulmi za su yi koyi da su. 602546