Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa, a wani rahoto da ya nakalto daga kamfanin dillancin labaran kur'ani na muzn an habarta cewa, ana ci gaba da gudanar da wani shiri na bayar da horon karatun kur'ani a salon kira'ar tartili a birnin Kutaif na kasar Saudiyya, wanda cibiyar kur'ani ta birnin ke aiwatarwa. Bayanin ya ci gaba da cewa horon da ake bai wa yaran ya takaitu ne kawai da lokacin bazaar, kuma ana lunka lokutan ta yadda za su iya koyon abubuwa da dama cikin kankanin lokaci. 602496