Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa, ya nakalto daga shafin yanar gizo na sadarwa nasij cewa, A cikin wata mai zuwa ne kwamitocin bitar alakoki tsakanin kasashen musulmi za su gudanar da zamansu a birnin Makka mai alfarma domin tattaunawa. Bayanin ya ci gaba da cewa kwamitocin za su gudanar da taron ne a dadidai lokacin da ake cika shekaru hamsin cur da kafa kwamitocin, wadanda suke tattauna muhimman batutuwa da suka shafi harkokin kasashen musulmi. 602466