Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa, a wani labari da ya samo daga shafin sadarwa na yanar gizo na isesco.org an habarta cewa, ana shirin gudanar da wani zaman taro a birnin Bruccel na kasar Belgium da nufin tattauna irin rawar da addinai za su iya takatawa a harkoki na kasa da kasa. Bayanin ya ci gaba da cewa kungiyar bunkasa al'adu da ilmomin addinin musulunci ta ISESCO ta shirya gudanar da zaman taron, wanda zai samu halartar masana daga sassa daban-daban na kasashen musulmi da ma na wadanda ba musulmi ba. 602409