IQNA

Za A Bude Asusun Tallafa Wa Cibiyoyin Kur'ani A Kuwait

15:50 - June 23, 2010
Lambar Labari: 1945467
Bangaren kasa da kasa; Daraktan banagren bincike kan ilmomin musulunci ta kasar Kuwait ya bayyana cewa za a bude wani asusun tallafa wa cibiyoyin kur'ani a kasar.
Kamfanin dillancin dillancin labaran iqna ya nakalto wani rahoto daga jaridar kasar Kuwait ta alanba cewa, Muhammad Alamiri daraktan banagren bincike kan ilmomin musulunci a ma'akatar kula da harkokin addini ta kasar Kuwait ya bayyana cewa za a bude wani asusun tallafa wa cibiyoyin kur'ani a kasar. Ya ci gaba da cewa za a kafa wannan asusu net a hanayar harhada kudaden zakka da kuma taimakon ma'aikatar kula da harkokin addini ta kasar, da nufin kara karfafa wadannan cibiyoyi da suke yada ilmin kur'ani a cikin kasar. 602390


captcha