IQNA

Jami'ar Azhar Ta Kasar Masar Za Ta Gudanar Da Gasar Kur'ani

15:51 - June 23, 2010
Lambar Labari: 1945469
Bangaren kasa da kasa; Jami'ar Azhar da ke birnin Alkahira na kasar Masar za ta dauki nauyin gudanar da wata gasar kur'ani da sunnar manzon Allah (SAW)
Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa, a wani labari da ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo na muhit an habarta cewa, jami'ar Azhar da ke birnin Alkahira na kasar Masar za ta dauki nauyin gudanar da wata gasar kur'ani da sunnar mason Allah tsira da amincin Allah su tabbata gare shi da alayensa. Rahoton ya ci gaba da cewa gasar za a gudanar da ita ne a bangarori daban-daban da suka hada da bincike kan tsarin kur'ani da kuma hikimomin da ke tattare a cikin ibarorinsa, kamar yadda gasar za ta hada bincike acikin sunnar mason Allah (SAW) kamar dai yadda majiyoyin jami'ar suka tabbatar. 602378
captcha