Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa, a wani labari da aka bayar a shafin sadarwa na yanar gizo na business24-7 an bayyana cewa, Abdulaziz algarir shugaban kungiyar majalisun dokokin kasashen musulmi ya bayyana cewa, wajibi ne kasashen musulmi su hada kansu domin fuskantar kalu balen gabansu. Ya ce idan aka yi la'akari da irin kalu bale dake gaban musulmi na harkokin tatatlin arziki da kuma siyasa, ya zama wajibi musulmi su hada kansu. 602264