Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa, babban sakataren kungiyar hadin kan kasashen msulmi Ihsan Auglo ya bukaci da a gudanar da bincike kan halin da musulmin kasar Chaina suke ciki domin taimaka musu. Ya ci gaba da cewa bisa la'akari da halin da musulmin kasar Chaina suka samu kansu a lokutan baya, kasantuwar su ne marassa rinjaye a kasar, hakan an bukatar a gudanar da bincike domin sanin halin da suke ciki yanzu, domin bas u taimakon da suke bukata. 602658