Bangaren adabi:an fitar da bayanin karshe na taron farko na kasa da kasa na marubuta na duniyar musulmi tare da kafa sakatariyar dindindim na wannan taro na birnin Tehran.
Cibiyar da ke kula da harkokin kur'ani a nan jamhuriyar Musulunci bayan ta nakalto daga majiyar labarai ta taron farko na taron kasa da kasa na marubuta na duniyar musulmi ta watsa rahoton cewa; an fitar da bayanin karshe na taron farko na kasa da kasa na marubuta na duniyar musulmi tare da kafa sakatariyar dindindim na wannan taro na birnin Tehran. Bayanin ya kara da cewa an samu sa hannun wakilan marubuta daga kasashe talatin da biyu na duniya da suka halarci wannan taro da suka yi nuni da kafa kungiyar kasa da aksa na duniyar marubuta a duniyar musulmi.
602386