Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa, tashar rasid ta bada rahoton cewa a cikin wata mai kamawa ne za a gudanar da wani taron adabi da rubutattun wakoki mai taken Imam Ali (AS) a garin Tarut na kasar Saudiyya. Bayanin ya ci gaba da cewa taron zai mayar da hankali kan wakokin da aka tsara kan amirul muminin Ali (AS) da ma sauran limaman gidan manzon Allah (SAW), wanda masana adabi mabiya mazhabar shi'a na kasar za su gabatar. Za a gudanar da zaman taron ne a daren maulidin Imam Ali (AS) a garin na Tarut. 603406